1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ba da rahoto game da yiwa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kwaskwarima.

Mohammad Nasiru AwalDecember 2, 2004

Rahoton da hukumar yiwa Majalisar Dinkin Duniya canje-canjen ta bayar bai burge ba kamar yadda masharhanta suka yi zato da farko.

Sakatare janar na MDD Kofi Annan da shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder a birnin Berlin
Sakatare janar na MDD Kofi Annan da shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder a birnin BerlinHoto: AP

Hukumar ba ta tabo batun da ya fi daukar hankali ba, wato yadda za´a tafiyar da shirin fadada yawan membobin kwamitin sulhu na MDD. Ko da yake membobin hukumar su 16 sun ba da shawarwari guda biyu kamar yadda yake kunshe a cikin ajanda, amma ba su yi karin bayani ba. Hakazalika ba su hakikance ba, bisa ra´ayin su kasar da ta fi cancanta ta samu kujerar dindin a kwamitin sulhu.

Ko shakka babu, hakan bai yiwa gwamnatin birnin Berlin dadi ba, wadda ba ta samu wani ci-gaba ba a kokarinta na samun zaunanniyar kujera a kwamitin sulhu. Yanzu dai ya zame mata dole ta kara mayar da himma wajen neman a kara yawan membobin masu kujerun dindindin da kasashe 6 kana kuma ta ba da hujjoji masu gamsarwa dangane da cancantar Jamus daya daga cikin wadannan kasashe da za´a daga matsayinsu a kwamitin sulhu. Kuma ko da yake kasashen Japan da Indiya da kuma Brazil na goya mata baya, to amma kowace daga cikin su na muradin samun kujerar dindindin a kwamitin sulhun. Yayin da su kuma a nasu bangaren kasashen Italiya da Pakistan da kuma Mexiko ke kokarin hana ruwa gudu. Alal misali Italiya ba zata yarda Jamus ta samu wannan kujera ba, yayin da Pakistan zata hau kujerar naki don hana Indiya samun kujerar, sannan ita kuma Mexiko zata nuna adawa da Brazil. A dangane da haka kasashen 3 suka ba da shawarar kirkiro sabbin kujeru 3 na wucin gadi da za´a kara musu wa´adi daga shekaru 2 zuwa 4.

Komin yawan kamfen din da shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder da ministan harkokin waje Joschka Fischer zasu yi game da muhimmiyar rawar da Jamus ke takawa a ayyukan wanzar da zaman lafiya a duniya ko kasancewarta kasa ta 3 a jerin kasashen da suka fi bawa MDD gudummawar kudi, ba zai yi wani abin a zo a gani wajen kara daga matsayinta don samun kujerar dindindin a kwamitin sulhu ba.

Ana iya kwatanta shawarar da hukumar ta bayar da cewa wani ci-gaba ne, domin hukumar ta yi kira da a nuna adalci wajen raba kujerun, ta yadda za´a shigar da nahiyoyin Afirka, Asiya da yankin kudancin Amirka a shirye-shiryen fadada kwamitin sulhu. To sai dai hakan ba zai yi wani tasiri ga matsayin kasashe 5 dake da kujerun dindindin a kwamitin ba, wato Amirka, Britaniya, Farsansa, Rasha da kuma China.

Wani abin da zai kawowa Jamus cikas kuma shine, tambayar da ake yi cewar me yasa kasashen Afirka zasu jinginar da bukatar neman kujerar dindindin don bawa wata kasar Turai damar samun wannan kujera? Hakazalika Jamus ba ta samun goyon bayan kasar Amirka, wadda har yanzu ba ta mance da adawar da Jamus din ta nuna da yakin da aka yi da Iraqi ba.

A daura da haka shawarar da kasashen Italiya da Pakistan da Mexiko suka bayar, zata fi burge kasashe masu kujerun dindindin, domin a hannu daya ba zata yi barazana ga matsayin wadannan kasashe ba kana a daya hannun kuma ta bawa sauran kasashe damar samun wakilci cikin kwamitin a lokuta da dama. Ga samun wata kujerar dindindin kam Jamus zata ci-gaba da yin mafarki har bayan taron babbar mashawartar MDD a cikin watan satumban shekara ta 2005, lokacin da za´a yanke shawara dangane da yiwa kwamitin sulhu garambawul.