An bada kyautar Nobel ta Chimestry
October 5, 2016An bada kyautar yabo ta Nobel ta binciken kimiyya da fasahar Chimestry ga wasu masana uku na kasar Faransa da Birtaniya da kuma Hollande kan aikin da suka yi na samar da karamin injin nukiliya.
Wadannan masana uku Jean-Pierre Sauvage na jami'ar Strasboug dan shekaru 71 a duniya da Fraser Stoddart na jami'ar Northwesten ta Amirka dan shekaru 74 da kuma Bernard Feringa na jami'ar Groningue ta kasar Hollande dan shekaru 64 sun samu kyautar saboda kokarin da suka yi na kera dan karamin injin nukiliyar wanda ke bada damar iya sarrafa nukiliyar ba tare da wata matsala ba.
Alkalan da suka bayar da kyautar Nobel din ga wadannnan masana sun ce aikin nasu zai taimaka a nan gaba ga kera sabbin na'urori da komfutoci kanana wadanda kuma ka iya daukar bayanai masu dinbin yawa fiye da na wannan zamani.