An bada sakamakon zaɓen raba gardama a Masar
March 20, 2011![](https://static.dw.com/image/6476435_800.webp)
Talla
Hukumomin shari´a a ƙasar Masar sun bayyana sakamakon zaɓen raba gardama da a aka shirya jiya Lahadi, domin kwaskwarima ga kundin tsarin mulki.
A cewar wani rahoto daga ma´ aikatar shari´a, kimanin kashi 70 ne cikin ɗari, na mutanen da su ka kaɗa ƙuri´a, su ka amince da saban kudin tsarin mulkin.
Jam´iyar ´yan uwa musulmi da jam´iyar PND ta hamɓararren shugaban ƙasa Osni Mubarack sun yi kira ga magoya bayansu su amince da wannan kudi.
A yayin da Mohamed El Baradei ɗan takara shugaban ƙasa mai buƙatar cenji ya nuna da shi.
Idan dai sakamakon ya tabbata, al´umar Masar za ta shirya zaɓen ´yan majalisar dokoki a watan Satumba na wannan shekara.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal