An bayar da kyautar Nobel ta kiwon lafiya
October 2, 2017An bayar da kyautar Nobel ta kiwon lafiya ga wasu likitikitoci uku da suka gudanar da wani aikin bincike kan tsarin aikin zuciya. Likitocin Jeffrey C. Hall da Michael Rosbash da Michael W. Young, sun yi nasarar tantance tsarin aikin da zuciya take yi a cikin sa'o'i 24 da kuma yadda bugawarta ke yin tasiri a rayuwar halittu a cikin yini da kuma a cikin dare.
Likitocin sun yi nasarar gano yadda bugawar da zuciya ke yi, ke daidaita bukatun barci da na abinci da kuma yanayin zafin jikin halittu. Likitocin uku sun samu tukuyci na kudi Euro dubu 937 na Euro da za su raba a tsakaninsu.
A shekara ta 2016 Yoshinori Ohsumi wani dan kasar Japan ne ya lashe kyautar Nobel din ta kiwon lafiya a sakamakon binciken da ya gudanar kan yadda kwayoyin hallittun dan Adam ke sabunta kansu lokaci zuwa lokaci.