1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An binne Paparoma Benedict na 16 a Vatican

Mouhamadou Awal Balarabe
January 5, 2023

An gudanar jana'izar tsohon Paparoma Benedict na 16 a dandalin St. Peter's da ke birnin Rome a karkashin jagorancin magajinsa Paparoma Francis, kuma a gaban dubun-dubatan mutane ciki har da shugabannin kasashe.

Beerdigung Papst Benedikt XVI
Hoto: Antonio Calanni/ASSOCIATED PRESS/picture alliance

An dora Bible a kan akwatin gawar Benedict na 16 kafin a bai wa limaman cocin Katolika damar yin bankwana da tsohon Paparoma, wanda ya rasu a ranar asabar da ta gabata. Daga bisa ne kuma aka binne shi PaParoma na farko da ya yi murabus a cikin karni shida, a wani kabari da ke cikin fadar Vatican.

Wannan dai shi ne karon farko cikin tarihin baya-bayannan da Paparoma mai ci ya halarci jana'izar magabacinsa. Baya ga shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier da shugaban gwamnatin tarayya Olaf Scholz da suka su halarci jana'izar, akwai tawaga daga mahaifar Benedict na 16 daga jihar Bavaria, karkashin jagorancin gwamna Markus Söder.

      

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW