1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An buƙaci a dakatar rikicin Siriya nan take

Usman ShehuApril 10, 2012

Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci a dakatar bude wuta Siriya nan take, domin kawo ƙarshen zubar da jini.

In this Sunday, April 1, 2012 photo, Free Syrian Army fighters train in a neighborhood of Damascus, Syria. Government and opposition forces clashed across Syria Monday as international envoy Kofi Annan prepared to brief the U.N. Security Council on the progress of his mission to ease the Syrian crisis. (Foto:AP/dapd)
Mayaƙan 'yan adawa a SiriyaHoto: AP

Wakilin MDD da ƙasashen Larabawa rikicin Siriya Kofi Annan ya buƙaci da a tsagaita wuta nan take a Siriya. Kofi Annan yace kada a yi wasti da shirinsa na dakatar da buɗe wuta. Kofi Annan yana magane ne a wani sansanin yan gudun hijiran Siriya dake cikin ƙasar Turkiya, inda yace hukumomin Damaskus na da lokaci nan da ranar Alhamis su yi aiki da starin da ya gabatar. Ko dayake hukumomin Siriya sun janye sojoji daga wasu sassan ƙasar, amma kawo yanzu hankali bai kwantaba, musamman inda masu neman kifar da gwamnati suka fi ƙarfi. A yan kwannan ne dai ake saran kwamitin sulhu na MDD zai yi zama kan lamarin. Masu neman kifar da gwamnatin Bashar Al-assad sun bada rahotonnin cewa har yanzu ana kai farmaki a biranen da suka fi ƙarfi, inda sukace aƙalla mutane 27 sun mutu. Rasha dai ta sake baiwa Siriya ƙarin wa'adi na yin biyya ga tsagaita wutan. Ita ma dai MDD a yammacin talata nan ta fidda sanarwar neman a tsagaita wuta nan take a rikicin na Siriya.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Zainab Muhammed Abubakar