1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An buda taron neman taimako ga Afghanistan a birnin London

January 31, 2006

Yau ne a birnin London na Britania a ka buda taron kasa da kasa na neman taimako ga kasar Afghanistan.

Wannan taro na yini 2, ya samu halartar shugaba kasar Afghanistan, Hamid Karzai ,da sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice, da sakartare Jannar na Majalisar Dinkin Dunia Koffi Annan, da mai masaaukin baki Tony Blair , da sauran wakilai na kasashen dunia kimanin 60.

A na sa ran sakamakon wannan taro, ya cimma nasara sa hannu, a kan wanni passali na mussamman, wanda zai tanadi farfado da kasar Afghanistan a tsawon shekaru 5 masu zuwa.

A yayin daya ke jawabin bude taron, Praminista Tony Blair, ya ja hankullan kasashen Dunia ,a kan mahimmancin bada taimako ga Afghanistan, da ke fama da yake yaken ta´andanci, ta hanyar hare haren yan Taliban da makamantan su.

Tunni, Sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice ta alkawarta cewa, Amurika a shire ta ke, ta bada tallafin dalla fiye da billiard daya, amma da sharadin amincewar majalisar Datawa.

Cemma kafin wannan taro, Amurika Amurika ta ware dalla billiard 6 ,domin taimakawa Afghanistan.