1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'umma sun halarci dandalin bikin Octoberfest a Munich

Zulaiha Abubakar
September 22, 2018

Rahotanni daga birnin Munchen na kasar Jamus sun bayyana yadda dubban al'umma suka yi turuwar shiga dandalin Oktoberfest a safiyar yau Asabar ganin bude gangar da ta kunshi wasu barasa kayan shan al'ummar kasar.

Start Oktoberfest 2018 ozapft
Hoto: Reuters/A. Gebert

Wannan biki da ake kira Oktoberfest wani fitaccen bikin gargajiya ne a Jamus in da mashaya barasa suke nuna gwanintar su a dandali tare da cin gasasshen nama, ana fara shagalin bayan magajin garin Dieter Reiter ya doki wata ganga da misalin karfe 12 na rana, sama da mutane miliyan shida ne dai ake sa ran zasu halarci bikin na bana, tun da fari an gudanar da hawan kilisa in da mata da maza suka yi shigar kayan gargajiya na mutanen Bavaria.

 

Ana fara bikin na Oktoberfest ne dai a makon karshe na Satumba sannan a kammala a ranar  bakwai ga watan Oktoba na kowacce shekara .