1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bude rumfunan zabe a Turkiyya

May 14, 2023

Al'ummar kasar Turkiyya sun fita kada kuru'u a zaben shugaban kasa da ka iya tsawaita wa'adin mulkin shugaba Recep Tayyip Erdogan da ya shafe tsawon shekaru 20 ya na mulki.

Hoto: Francisco Seco/AP Photo/picture alliance

Wannan dai zaben shi ne mafi kalubale ga Recep Tayyip Erdogan mai shekaru 69 ke fuskanta yayin da ake kallon zaben a matsayin mai mahimmanci.

Jagoran adawa, Kemal Kilicdaroglu da ke fatan kai gwamnatin Erdogan kasa dai, na da goyon bayan jam'iyyun adawa shida. A hannu guda kuma Erdogan ya sanya kafa ya shure rade-radin da ake na cewa, ba zai mika mulki ba in har bai yi nassara a zaben ba.

A kalla mutane miliyan 61 ne ake sa ran za su fito zaben ciki har da miliyan 5 da wannan ne karonsu na farko na kada kuru'a. Tuni dai Turkawa da ke kasashen ketare suka kada nasu kuru'un.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW