An fara kada kuri'ar zaben shugaban kasa a Uganda
January 15, 2026
Rahotannin farko na cewa an yi jinkirin bude rumfunan zabe, kamar yadda aka saba a kasar Uganda, amma an fara kada kuri’a jim kadan bayan karfe 7 na safe a wata unguwa da ke birnin Kampala, kamar yadda ‘yan jaridar AFP suka gani. An baza 'yan sanda da sojoji da ke sintiri a garin Jinja da ke kan iyaka, in ji wata tawagar AFP.
Uganda na gudanar da zeben ne cikin yanayi na rashin Intanet a fadin kasar da kashi 70 cikin 100 matasa ne 'yan kasa da shekaru 35, yawan rashin aikin yi shine babban batu ga masu jefa kuri'a na farko a 2026.
Gwamnati ta katse Intanet gabannin ranar zabe don hana yaduwar labaran karya da rage kaifin masu tada zaune tsaye a lokcin zabe da kuma bayan zabe. Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa kan matakin.
Zaben zai fi zafi ne tsakanin Shugaba Museveni mai shekaru 81 da fitaccen dan siyasa Bobi Wine mai shekaru 44, wanda ya sha zargin hukumomin Uganda da kawo cikas a gangamin yakin neman zabensa.
Akwai sauran 'yan takara guda shida a zaben na bana, ciki har da fitaccen lauya Nandala Mafabi mai shekaru 59, ya ja hankalin jama'a da dama a sassan kasar Uganda, inda ya yi alkawarin sarrafa albarkatun kasar cikin tsanaki tare da yakin neman zabe mai taken, "Gyara tattalin arziki don samar da kudi a aljihunmu."
Cin hanci da rashawa da rashin aikin yi su ne kan gaba cikin manyan matsalolin masu zabe a Uganda. Alkaluman hukumar kididdiga ta kasar na watan Satumban 2025, sun nuna kusan rabin matasan kasar masu shekaru 18 zuwa 30, ba su da aikin yi, ba su da ilimi.