An buda runfunan zaben rabagardama a Burtaniya
June 23, 2016Talla
Tun shekaru da dama ne masu adawa da kasancewar kasar ta Burtaniya cikin Tarayyar Turai ke ta nema da a yi wannan zaben raba gardama, wanda kuma a baya Firaministan kasar David Cameron ya sha alwashin gudanar da shi.
Wannan zabe dai zai taka babbar rawa kan makomar siyasar kasar ta Burtaniya, da ma ta Tarayyar Turai, wanda ake ganin idan har masu ra'ayin ficewa suka yi rinjaye, to kasar ta Burtaniya da Tarayyar Turai za su shafe tsawon shekaru wajen tattauna matakan wannan rabuwa mai cike da sarkakiya.