An bude taron koli na kungiyar AU
February 17, 2024Talla
Shugabannin kasashen Afirka sun bude taron na 2024 a daidai lokacin da nahiyar ke fama da matsalolin juye-juyen mulki da tashe-tashen hankula da rikice-rikicen siyasa da ma na rashin tsaro da hauhawar farashin masarufi. An kuma gudanar da wani taron a rnar Juma'a a a gefen taron kolin na Kungiyar Tarayyar Afirka AU, domin samun hanyoyin sake wanzar da zaman lafiya a gabashin Jamhurinyar Dimokradiyar Kwango.
Kasashen Gabon da Nijar ba za su halarci taron ba sakamakon dakatar da su daga kungiyar saboda juyin mulkin da sojoji suka yi. Kazalika hakan take ga kasashen Mali da Guinea da Sudan da kuma Burkina Faso. Ko baya ga matsalolin da nahiyar ke fuskanta, ana sa ran taron ya tattauna batun rikicin Zirin Gaza.