An bude taron kolin kasashen Musulmin duniya a Turkiyya
April 14, 2016Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bude taron kolin kungiyar kasashen Musulmin Duniya OIC tare da yin kira da a yaki mayakan sa-kai. A lokacin da yake jawabi a gaban shugabannin kasashen Musulmi da ke halartar taron na karo 13 ja birnin Santanbul, shugaba Erdogan ya ce ya kamata kasashen yamma sun hada kai da kasashen duniyar Musulmi wajen yakar kungiyoyin 'yan ta'adda, sannan ya yi kira ga kasashen Musulmi da su goyi bayan wani yunkurin kasar Saudiyya kuma su amince da kafa wani kawancen yaki da tarzoma.
"Ya kamata mu mara wa shirin kafa kawancen kasashen Musulmi na yaki da ta'addanci baya, maimakon mu rika jiran wasu kasashe da nufin kawo mana daukin yaki da tarzoma da sauran rigingimu da ke faruwa a kasashen Musulmi. Dole ne mu magance matsalolin da kanmu."
Erdogan ya ce abin kunya ne kasancewa akasarin bakin haure da 'yan gudun hijira da ke kokarin shiga Turai, Musulmi ne.