1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sanya AU a cikin kungiyar G20

September 9, 2023

Shigar da kungiyar Tarayyar Afirka da aka yi a cikin kungiyar ta G20 ka iya sauya sunan kungiyar zuwa G21.

Hoto: via REUTERS

Shugabannin kungiyar G20, mallakin manyan kasashen duniya masu karfin tattalin arziki sun fara taronsu na shekara-shekara a wannan Asabar a birnin New Delhi na kasar Indiya.

Babban abin da ya dauki hankali a wurin bude taron shi ne sanya kungiyar tarayyar Afirka ta AU da aka yi a cikin kungiyar. Shugaban kungiyar ta AU, Azali Assoumani ya halarci taron domin alamta shigar da Tarayyar Afirka da aka yi a matsayin mamba ta dindin a kungiyar ta G20.

Firaministan Indiya Narendra Modi ya yi jawabin maraba ga shugabannin duniya da ke sa ran taronsu kwanaki biyu ya tattauna batun yakin Ukraine da sauyin yanayi a duniya.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani