1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AN BUDE TARON NEPAD A KENYA

JAMILU SANIOctober 29, 2003

A kasar Kenya yau laraba aka bude baban taron kungiyar habaka tattalin arzikin kasahen Africa ta NEPAD,a yayin wanan taro ne ake sa ran ministoci 11 da suka fito daga gabashin Africa zasu tattauna yadda za'a bulo da matakan yaki da kaangin talaucin da ake fama da shi a nahiyar Africa,tare kuma da samar manufofin da zasu taimaka wajen matsaloli na koma bayan tattalin arziki da ake fama da shi a nahiyar Africa baki daya.
Shugbanin kasashen Africa uku suka sami damar halartar baban taron na kungiyar habaka tattalin arzikin kasahen na Africa da suka hadar da mai masaukin baki shugban kasar Kenya Mwai Kibaki da kuma takwarorinsa na Uganda da kuma Ruwanda Paul Kagame da kuma Yoweri Musevni. Haka zalika wasu kasahen na Africa da suka hadar da Burundi,Dijibouti,Eritrea,Ethopia,Maritius Somalia,Tanzania da kuma Sudan,sun aika manyan jami'an gwamnatocin kasahen su,don su wakilci kasahen su a yayin baban taron na NEPAD da aka fara shi yau laraba a kasar Kenya. A shekara ta 2001 ne dai wasu shugabanin kasahen Africa suka kafa kungiyar habaka tattalin arzikin kasahen Africa ta NEPAD,don hakan ya taimaka wajen habaka harkokin zuba jari,da kuma samun sasauci na bashi da suka ciwo daga ketare,tare kuma da ganin cewa kasahe masu arzikin masana'antu sun bude kofofin kasuwanin su ga kasahe masu tasowa na Africa. Wata manufar kuma ta kafa kungiyar ta NEPAD shine,samar da kyakyawan shugabanci a nahiyar Africa ta hanyar tabatar da kyakyawan tsari na democradiya,tare kuma da samar da manufofi da zasu taimaka wajen habaka tattalin arzikin kasahen nahiyar Africa baki daya.
Ministan Tsare tasre na kasar Kenya Peter Anyang Nyong,ya baiyana cewa a yayin taro na NEPAD za'a fi mayar da hakalin wajen yin nazari game da rahotanin da ministocin kasahe suka gabatar,daga bisani kuma a samar da ingantatun manufofin da zasu taimaka wajen ciyar da kungiyar ta NEPAD gaba.
Ministan tsare tsaren dai na Kenya,ya kara da cewa tun lokacin da wasu kasahen Africa suka sami yancin kansu daga turawan mulkin malakar yammacin Turia har kawo yanzu babu wani cigaba na na ku zo mu ganin da suka samu a fusakar cigaban tattalin arzikin kasa.
Da yake jawabinsa na bude taron na NEPAD mukadashin shugaban kasar Kenya Moody Awori,amfani da wanan dama yayi wajen jan hankalin shugabanin kasahen Africa da su mayar da hankali wajen bunkasa harkokin zuba jari na kamfanonin gida da waje,don ta haka ne za'a sami bunkasar tattalin arziki a nahiyar Africa. Daga cikin mahalarta taron na NEPAD har da sakatarorin kungiyar hadin kann kasahe ta (IGAD)da kuma da harkokin kasuwanci ta a gabashi da kuma kudancin Africa ta (COMESA).