1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bude tashoshin kada kuri'a a zaben Jamus

Abdullahi Tanko Bala
September 22, 2017

A ranar Lahadi ce Jamusawa ke zaben 'yan majalisar dokoki na tarayya ta Bundestag. Duk da cewa jam'iyyar Angela Merkel za ta iya samun rinjaye, amma jam'iyyar AfD mai kyamar baki za ta iya samun wakilci a majalisar.

Deutschland Plakate Bundestagswahlen 2017
Hoto: Getty Images/S. Gallup

Idan dai kuri'ar jin ra'ayi abin gasgatawa ne, to Jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnati Angela Merkel za ta lashe zaben da za'a yi a ranar Lahadi. Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta baya-bayan nan ta nuna jam'iyyar CDU na iya samun kusan kashi 36 cikin dari na kuri'iun da za'a kada. To amma kuma a waje guda kuri'ar jin ra'ayin ta nuna Jamusawa da yawa har yanzu basu yanke shawarar jam'iyyar da za su zaba ba. A saboda haka shugabar gwamnati Angela Merkel, a zagayen karshe na yakin neman zaben da ta gudanar a wannan makon ta ce har yanzu ba za'a iya yanke hukunci a kan zaben ba tukunna.

Merkel da jam'iyyarta ta CDU na shirin darawa a zaben 2017Hoto: imago/photothek/T. Imox

  Angela Merkel ta ce "Muna cikin yanayi mai sarkakakiya, saboda haka bama bukatar gwaji abin da muke bukata shine tabbacin zaman lafiya, kwanciyar hankali da tsaro. Kuma karfin ikon yana kan gwamnatin tsakiya wato tarayya, a saboda haka kowace kuri'a da za'a kada a ranar Lahadi tana muhimmanci"

A bisa al'ada babu jam'iyyar da ke samun rinjaye dari bisa dari da za ta iya kafa gwamnati ita kadai. A saboda haka sai Jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ta nemi abokiyar kawance ko da kuwa ita ce ta kasance akan gaba. Shekaru hudu da suka wuce kawancen CDU da SPD ne suka yi gwamnatin hadaka. Kuri'ar jin ra'ayin jama'a dai ta yi hasashen cewa Jam'iyyar ta SPD za ta sami kashi 21 zuwa kashi 23 ne cikin dari. Shugaban jam'iyyar Martin Schulz ya dage cewa yana so ya zama shugaban gwamnati na gaba.

 Martin Schulz ya ce "Angela Merkel ta gudanar da mulkiin Jamus bisa taken " kasar da muke ciki kuma muke son mu yi rayuwa mai kyau a cikinta" Ta yi gaskiya. Muna rayuwa mai kyau kuma muna jin dadin zama a cikin kasar nan. Amma kuma muna son rayuwa mai kyau a gaba, shi ya sa nake cewa muna bukatar baiyanawa jama'a wane tafarki ne muke dauka kuma ina muka dosa?."  

Schulz na kokarin rata tsakanin jam'iyyarsa SPD da ta MerkelHoto: Reuters/W. Rattay

'Yan jam'iyar ta Social demokrats dai basu bayyana ko suna da sha'awar shiga sabuwar kawance domin kafa gwamnatin hadin gambiza da CDU idan suka zo na biyu ba. Kananan jam'iyyu ka zama 'yan sarki. A Jamus jam'iyya na iya tura wakilai zuwa majalisar tarayya ta Bundestag idan ta sami akalla kashi biyar cikin dari na kuri'un da aka kada a kasa baki daya.

A halin da ake ciki akwai kananan jam'iyyu guda biyu a majalisar dokokin a yanzu. Jam'iyyar Die Linke ta 'yan mazan jiya da kuma Greens mai rajin kare muhalli. Sabuwar majalisar ta kunshi jam'iyyu guda shida. Kuma kuri'ar jin ra'ayi ta nuna jam'iyyar FDP mai rajin ci gaban kasuwanci tana da kyakkyawar dama ta sake komawa majalisa bayan ficewa da ta yi sakamakon shan kaye a zaben 2013.

Kuma a karon farko tun bayan yakin duniya na biyu jam'iyyar masu tsattsauran ra'ayin rikau za su shiga majalisar. Jam'iyyar kuwa ita ce AfD wadda ta kaddamar da yakin neman zabe da kakkausar adawa da yan gudun hijira. Alexander Gauland shine jagoran yan takarar jam'iyyar.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani