1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara zabe a kasar Zimbabuwe

Yusuf Bala Nayaya
July 30, 2018

Mutanen kasar Zimbabuwe sun fita kada kuri'a a zaben shugaban kasa a karon farko ba tare da tsohon Shugaba Robert Mugabe ba a matsayin wanda yake jagorancin kasar da ke yankin kudancin Afirka.

Simbabwe Präsidentenwahl
Hoto: Reuters/M. Hutchings

Yayin da 'yan takara 23 ke neman shugabancin kasar a Zimbabuwe 'yan takara biyu su ake tsammanin daya ya kai labari, Nelson Chamisa dan shekaru 40 matashi daga jam'iyyar MDC mai adawa da Shugaba Emmerson Mnangagwa dan shekaru 75 da ya gaji Mugabe a karagar mulki.

Wannan zabe dai ana ganin za a fafata sosai tsakanin wadannan 'yan takara ganin yadda kuri'ar jin ra'ayin jama'a a makon da ya gabata ta nunar da cewa Mnangagwa da aka fi sani da "Kada" ko  "The Crocodile" a Turance ya bai wa Chamisa rata ta kashi uku ne cikin dari kacal.

Tun da misalin karfe bakwai, biyar ke nan agogon GMT aka bude tashoshin kada kuri'ar yayin da ake sa rai mutane milyan biyar za su yi zabe don neman shugabanci da zai iya fitar da kasar daga yanayi na tabarbarewar tattalin arziki.