1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta tsoratar game da illolin wasu kasuwannin Chaina

Zulaiha Abubakar
April 23, 2020

Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo, ya ja hankalin mahukuntan Chaina su rufe kasuwannin namun daji bayan ya danganta cigaba da gudanar da irin wadannan kasuwanni da billar cututtuka masu wahalar magani.

Smbolfoto Illegaler Gürteltier-Handel in
Hoto: AFP/G. Ginting

Sabuwar cutar ta COVID-19 dai, ta samo asali ne daga wata kasuwar namun daji dake birnin Wuhan na kasar ta Chaina a shekarar bara. Annobar Corona Virus ta karade duniya cikin kankanin lokaci tare kashe mutanen da yawansu ya kai 180,000 bayan jikkata sama da mutane miliyan biyu a kasashe daban-daban, mumunan ibtila'in da ya haifar da tsaiko a kowanne bangare.