SiyasaAfirka
Majalisar Dinkin Duniya ta nemi kawo karshen yakin Libiya
October 5, 2020Talla
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci manya kasashen duniya da ke da su karfi da karfe wajen ganin an tsagaita wuta a yakin basasar kasar Libiya, sakataren ya jaddada cewa makomar kasar ta Libiya na cikin hatsari.
Majalisar ta Dinkin Duniya hadin gwuiwa da kasar Jamus sun shirya wani taro na wuni daya domin lalubo bakin zaren rikicin na Libiya, inda aka tattauna batun yadda bangarorin da basu ga maciji da juna gami da 'yan koransu suka yi fatali da takunkumin shigowa da makamai a kasar.
Kasar ta Libiya dai ta tsunduma cikin rikici ne bayan da wani yunkurin da ya samu goyon bayan kungiyar tsaro ta NATO ya hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Muammar Gadhafi.