An bukaci yin zaben na gari a Zambiya
November 11, 2014Kungiyar ta fidda wannan sawarwar yayin da ake yin jana'izar tsahon shugaban kasar ta Zambiya Micheal Sata, wanda ya rasu makwanni da suka gabata. Shugabar hukumar Tarayyar Afirka Nkosazana Dlamini-Zuma, ita ce ta yi kiran gudanar da zaben mai inganci, yayin da take magana wa dubban wadanda suka taru lokacin yin ban kwana da gawar marigayi Shugaba Sata.
Bayan rasuwar Micheal Sata an mika wa mataimakinsa Guy Scott da ya jagoranci gwamnati kafin kamar yadda dokar kasar ta tanada. Anan dai saran gudanar zaben shugaban kasar a watan junairun badi. Amma dokar kasar ta haramtawa shugaban mai rikon Guy Scott tsayawa takara domin ance sai wanda aka haifi iyayensu a kasar ta Zambiya zai iya yin takara, shi kuwa Scott an haifi iyayen shi ne a kasashen waje.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Suleiman Babayo