An cafke mataimakin kungiyar Boko Haram a Najeriya
April 3, 2016Kazalika Khalid al-Barnawi wanda kuma ke zama daya daga cikin mutane uku da mahukuntan Amirka suka zayyana sunayen su a shekara ta 2012 a matsayin futattun 'yan ta'adda.
Mai magana da yawun rundunar sojojin Najeriya Brigediya Janar Rabe Abubakar shi ne ya bayyana hakan, a inda ya kara da cewar jami'an tsaron sun sami nasarar cafke shi ne a ranar juma'ar nan a garin Lokoja da ke cikin jihar Kogi a Arewacin Najeriya.
Shi dai Kahalid al-Barnawi da ke zama mataimakin Shugaban kungiyar Boko Haram na daya daka cikin futattun jerin mutanen da rundunar sojojin Najeriya take nema ruwa a jallo a yakin da suke na kakkabe masu ayyukan kungiyar Boko Haram.
Cafke jagoran Ansarun ya sake karfafawa jami'an Najeriyar kwarin gwiwa a yakin da suke da kungiyar Boko Haram wanda hakan ke zama nasarar baya bayan nan da rundunar sojojin ke cigaba da samu a duk fadin kasar.