1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanci

Hukumomin tsaron Birtaniya sun cafke maharin ta'addanci

Suleiman Babayo
August 14, 2018

Jami'n tsaron Birtaniya sun cafke wani matashin da ya kai harin ta'anci da mota inda ya jikata mutane da dama lokacin da ya buga motar da shingen tsaron majalisar dokoki a birnin London.

Mann fährt mit Auto in Absperrung vor Londoner Parlament
Hoto: picture-alliance/AP Photo/ITN

'Yan sanda a birnin London na Birtaniya sun cafke wani matukin mota da ya kara motarsa a jinkin shingen tsaron majalisar dokoki cikin wani yanayin harin ta'addanci inda wasu da ke wucewa suka samu raunika. An kai hari kusa da inda aka halaka mutane biyar cikin wani harin na ta'addanci a shekarar da ta gabata ta 2017.

Jami'an 'yan sanda sun ce maharin yana cikin shekarunsa na 20, kuma ba ya bayar da hadin kai a cikin binciken da ake yi. Sai dai babu wata shaidar cewa yana da dangantaka da wata kungiyar 'yan ta'adda. Mahukunta a kasar Birtaniya suna kara harama kan dakile duk wani yunkurin harin ta'addanci.