'Yan sanda sun kama wasu 'yan Kaar Jamus a Masar
January 11, 2019Talla
Wasu majiyoyin tsaro na Masar sun ce tuni da aka fara kokarin sake tisa keyar matasan zuwa Jamus. Na farko wanda aka kama Mohammed A dan shekaru 24 an kamashi ne a cikin watan Disamba da ya gabata a filin saukar jiragen sama na birnin Alkahira. Yayin da na biyu wanda dan shekaru 18 ya kai ziyara ganin kakansa a cikin watan Disamba bara a birnin Alkahira amma kuma tun lokacin bai sake komawa Jamus ba.