An cafke 'yan adawa a Zambiya
August 16, 2016'Yan sandan Zambiya sun ce sun damke 'yan adawa 150 dangane da zanga-zangar da ta barke bayan da aka baiyana shugaba Edgar Lungu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar.
Magoya bayan dan takarar adawa Hakainde Hichilema sun bazama a kan tituna a gundumar kudancin kasar bayan baiyana sakamakon zaben a ranar Litinin inda suka rufe hanyoyi da kuma kona tayoyi. A cikin wata sanarwa da kwamishinan 'yan sandan gundumar Godwin Phiri ya fitar ta ce mutanen kudancin gundumar sun yi tsammanin Hichilema ne zai ci zabe a saboda haka wannan ya haifar da tarzoma abin da kuma ya kai ga cafke mutanen 150. Hichelema dan takarar Jam'iyyar UPND ya yi watsi da sakamakon zaben yana mai cewar an tafka magudi ya kuma sha alwashin kalubalantar sakamakon a kotu.