1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ceto daliban sakandaren Kankara

December 18, 2020

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya ce illahirin yaran da aka ceto na karkashin kulawar jami'an tsaro yayin da kuma ake duba lafiyarsu gabanin hannanta su ga iyayensu.

Nigeria Katsina | Kankara | Angriff auf Schule
Hoto: Abdullahi Inuwa/REUTERS

Kimanin yara sama da dari uku ne gwamnatin jihar Katsina da ke Arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta ceto su daga hannun masu garkuwa da mutane. Gwamnan jihar Alhaji Aminu Bello Masari ya ce illahirin yaran na karkashin kulawar jami'an tsaro yayin da kuma ake duba lafiyarsu gabanin hannanta su ga iyayensu. Sai dai abin da ba a tabbatar da shi ba shi ne gaba daya yaran ne aka ceto ko akwai saura tare da sanin an biya kudin fansa ko ko a'a ba.

Shugaba Muhammadu Buhari a na sa bangaren ya yaba da wannan ci gaba da aka samu, wanda ya bayyana da wani abin sanyaya zuciya ga iyayen yaran da ma kasa baki daya. Yankin na Arewa maso yammacin Najeriya inda shugaban ya fito ya jima ya na fama da hare-haren masu satar shanu da ma satar mutane tare da yin garkuwa da su domin neman kudin fansa.