An gano 'yan Thailand da suka bace a Kogo
July 2, 2018Talla
Masu ayyukan ceto sun ce dukkannin wadanda aka samu suna raye, kuma tuni aka tura jami'an kiwon lafiya domin duba lafiyarsu tare da tabbatar da basu dukkannin kulawar da suke bukata cikin gaggawa.
Hukumomin gwamnatin yankin da hatsarin ya faru a arewacin Thailand da ke makotaka da kasar Myanmar, sun bada tabbacin yashe ruwan da ke cikin Kogon domin samun damar ceto sauran mutane da kuma kauce wa fadawa irin hatsarin a nan gaba.