Mutane 27 sun kubuta daga masu garkuwa a Najeriya
May 9, 2019Talla
A cikin wata sanarwar da rundunar 'yan sandan suka fitar, sun ce mafi yawan wadan da aka kubutar 'yan jihar Zamfara ne da ke arewa maso yammacin kasar. 'Yan sandan sun tabbatar da bindige biyu daga cikin masu garkuwan.
Nasarar kubutar da mutanen ta zo ne a dai dai lokacin shugaban 'yan sandan Najeriyar Mohammed Abubakar ya kaddamar da sabbin dabarun tinkarar ayyukan ta'addanci da masu satar mutane a kasar.
Rahotannin jami'an 'yan sandan Najeriya na cewa cikin watanni hudun farko na shekarar 2019, mutane 270 ne aka kama bisa zargin satan mutane domin samun kudin fansa.