An ceto mutane 360 da Boko Haram suka sace a Borno
June 7, 2026
A wata sanarwa da sojojin suka fitar sun ce sun samu nasarar kubutar da mutanen da galibinsu mata da kananan yara a dazukan da ke tsaunukan Mandara. Mai magana da yawun sojojin Haruna Sani, ya ce yara biyu sun rasa rayukansu, sakamakon yanayin da suka tsinci kan su cikin tsaunuka na tsawon kwanaki.
Karin bayani:Kawancen sojojin Amurka da Najeriya sun kashe kwamandan IS
Sani ya kara da cewa, an kai sauran mutanen da aka ceto wani kebantaccen wuri, domin a duba lafiyarsu da kuma basu kulawa ta musamman. Ya ce nasarar da suka samu wata koma baya ce ga kungiyar Boko Haram.
Karin bayani:Yaushe za a samu tsaro a Bornon Najeriya?
Najeriya dai na fuskantar kalubalen tsaro mafi girma musamman a shiyyar arewa, inda kungiyoyin 'yan ta'adda daban-daban ke garkuwa da mutane domin su karbi kudin fansa. Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana ce dubban mutane suka mutu a kasar sakamakon ayyukan 'yan ta'adda.
.