An ceto wasu baƙin haure a kusa da gaɓar tekun Libiya
May 2, 2015Talla
Jirgin ruwan na gadin teku da Ƙungiyar Tarrayar Turai ta tura a tekun na Bahrum domin yaƙi da lamarin baƙin haure, ya ceto 'yan cirani kusan 217 a kusa da gaɓar tekun Libiya.
jami'an sun ce sun kame wasu mutane biyu matuƙa jirgin waɗanda suka ce za su miƙasu ga jam'ian tsaron Italiya.Yawanci fasinja da ke cikin jirgin 'yan ƙasashen Yankin Kudu da Hamada ne.