SiyasaJamus
An ceto wasu bakin haure a Italiya
January 22, 2022Talla
Masu gadin kan teku a Italiya, sun ceto wasu bakin haure sama da 300 wadanda ke kan hanyarsu ta neman shiga nahiyar Turai ba bisa ka'ida ba.
Jirgin ruwa da ke dauke da mutanen da galibin su suka fito daga kasashen Afirka da ma wasu na Asiya, ya fusknci matsala a tsibirin Lampedusa.
Daga cikin wadanda aka ceto dai har da mata 17 da kananan yara shida.
Masu gadin na kan tekun, sun shaidar da samun matsalolin a kokarinsu na ceto mutanen saboda yawan su da kuma kankantar jirgin da ya kwaso su.
Sun ma ce mutanen na gab da fuskantar hadarin nitsewa saboda fashewar jirgin ka iya yi.
Kungiyar likitoci masu ba da agaji ta Doctors without Borders, ta ce jirgin na dauke ne da bakin haure 430.