1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ceto wasu bakin haure a Sahara

July 17, 2023

Jami'an da ke gadin kan iyaka a Libiya, sun ceto wasu bakin haure 'yan asalin kasashen Afirka bakar fata wadanda hukumomin Tunisiya suka tasa keyarsu zuwa gida.

Hoto: Mahmud Turkia/AFP

Jami'an na Libiya dai sun gano tarin bakin hauren ne a cikin dazukan Sahara, inda suka kwashe su zuwa kauyen al-Assah.

Wasu mutum biyu daga cikin bakin hauren da asalinsu 'yan Najeriya ne, sun ce wasu sojojin kasar Tunisiya sun lakada musu duka tare da korar su zuwa dazukan domin ganin su koma iyakar Libiya.

A ranar Lahadi ne dai gwamnatin Tunisiya ta sanya hannu kan wata yarjejeniya da Tarayyar Turai kan batun hana shigar bakin haure da ke bi ta kasar.

Wasu ma sun yi zargin sojojin na Tunisiya da kona musu takardunsu na Fasfo, kafin shake wasu mutum 35 daga cikin su cikin wata mota zuwa kan iyakar ta Libiya.