An ceto 'yan ci rani a Sahara
May 4, 2014Baƙin haure, da masu ikirarin yi musu jagora, suka barsu a tsakiyar dajin Sahara, a halin yanzu an isa da su zuwa birnin Dongola da ke da nisan km 500 a arewa maso yammacin Khartoum babban birnin Sudan.
'Yan ci ranin, a ƙalla 600 mata da ƙananan yara, sun kasance mafi yawan su 'yan ƙasashen Habasha da Sudan, inda kwanaki huɗu da suka gabata ma fiye da mutane 300 ne baƙin hauren, masu yi musu jagora suka barsu tsakanin Sudan da Libiya wanda a ciki mutane guda goma suka mutu. Mutanen dai na kan hanyar su ne ta zuwa Libiya a lokacin da lamarin ya afku. Dama dai akasari masu wannan sana'a ta yi wa baƙin haure jagora dan ketarar da su, suna barin su ne a cikin Sahara bayan kuma sun biya su kuɗaɗen yin hakan.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Abdourahamane Hassane