1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Russland Syrien-Resolution

December 16, 2011

Bisa ga dukkan alamu kawayen Siriya irinsu Rasha sun fara gajiya da halin tashin hankal da zubar da jini dake faruwa kasar, inda yanzu Rasha ta fidda wani kuduri kan Siriya a MDD

Men raise their shoes as a sign of disrespect during a protest demanding the release of Syrian refugee Ahmed al-Shureiqi in front of the Syrian Embassy in Amman, Jordan, Sunday, Dec. 11, 2011. The Syrian Embassy says a dozen of its nationals living in Jordan have beat up consulate employees, wounding at least two diplomats and several others, including a Syrian security guard. An Embassy statement says its guards have arrested one of the attackers, identified as Syrian refugee Ahmed al-Shureiqi. (Foto:Mohammad Hannon/AP/dapd)
Masu adawa da gwamnatin Siriya ke boreHoto: dapd

Bayan jan kafa da hana-ruwa-gudu na watanni da dama, abin da ya hana yin Allah wadai da Siriya a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya, Rasha yanzu dai akwai alamun ta shirya kara tsananta matsin lamba kan gwamnatin shugaba Bashar al-Assad. Rasha din, dake da ikon hawa kujerar naki a kwamitin, ta gabatar da daftarin wani kudiri a game da rikicin kasar ta Syria. Amerika da Jamus sun yi marhabin da wnanan mataki na Rasha, inda suka kwatanta shi a matsayin abin da zai taimka domin kawo karshen banbancin dake tsakanin kasashe a kwamitin na MDD, yadda za'a sami nasarar kawo karshen halin da ake ciki mai wahala a Syria.

Duk da hakan, kasashen na Jamus da Amirka sun baiyana bukatarf ci gaba da tattaunawa a game da yadda kwamitin sulhun na majalisar dinkin duniya zata maida martanin da ya dace gameda halin da ake ciki a Syria. Kasashen kungiyar hadin kan Turai da suka hada har da Faransa da Ingiola da Jamus sun sami nasarar tabbatarda ganin shugaban hukumar kare hakkin yan Adam ta majalisar dinkin duniya, Pillay ta baiyana gaban kwamitin sulhun, inda ta sanarwa wakilai game da mummujnan halin da ake ciki a kasar ta Syria. Wannan bayani nata da mafi yaawan wakilan kwamitin suka baiyana shi a matsayin mai matukar muni, da alamu ya ja hankalin Rasha ta janye matakin ta na hana ruwa gudu kan kasar ta Syria a kwamitin. Jakadan Rasha a majalisar dinkin duniya, Vitali Tschurkin ranar alhamis a wani yanayi na ba-zata, ya gabatarwa wakilai daftarin wani kudiri kan kasar ta Syria.

Zanga-zangar yan Siriya masu goyon bayan Bashar al-AssadHoto: picture-alliance/dpa

"Yace muna gabatarwa kwamitin sulhu wata sabuwar shawara, wadda zata kula da halin fda ake ciki a baya-bayan nan da kuma yan watannin da suka wuce, wadda kuma zata kara karfafa dukkanin bayanan dake kunshe a kudirorin da aka sha gabatarwa a can baya, game da bukatar kawo karshen tashin hankali da bukatar kiyaye manfofi na kare hakkin yan Adam da kuma bukatarf hamzarta aiwatar da gyare-gyare"

Kudirin na Rasha zai kuma yi Allah wadai da dukkanin bangarorin dake amfani da karfi kan al'ummar Syria, sai dai kuma bai yi magana game da dorawa kasar ta Syria sabon takunkumi ko tsananta wadanda ke kan ta ba.

Wannan mataki na Rasha ya sami marhabin daga wakilan kungiyar hadin kan Turai, ko da shike sun baiyana bukatarf ci gaba da tataunawa. Jakadan Faransa a majalisar dinkin duniya, Gerard Araud ya kwatanta sabon kudirin na Rasha a matsayin abu mai ban mamaki, to amma ya kara da cewar wannan kudiri saboda rashin daidaituwar sa, ana bukatar yi masa gyara mai tsanani. Haka nan shima wakilin Jamus a majalisar Peter Wittig irin wannan ra'ayi ya baiyana, ko da shike yace kudirin wani matakine na neman dinke barakar dake tsakanin wakilan kwamitin sulhun game da rikici kasar Syria.

Yan adawan Siriya yayin ziyarar da suka kai kasar RashaHoto: dapd

Sakatariyar harkokin wajen Amerika, Hilary Clinton, tace ya kamata ayi taka tsan-tsan a gameda daftarin kudirin na Syria.

Tace "ko da yake ban ga daftarin kudirin na Rasha ba, in banda dan gajeren bayani da aka yi mani game dashi, amma da alamu akwai fannoni da dama cikin sa da ba zamu amince dasu ba. Har yanzu akwai banbanci tsakanin gwamnati da masu zanga-zanga cikin lumana da kuma sauran yan Syria dake kkarin kare kansu ne kawai. TO amma zamu yi nazarin wnanan kudiri a tsanani. Tilas ne kuma ra'ayin mu ya daidaita da na kungiyar hadinkan Larabawa wadda ta kasance kan gaba a wajen maida martani kan abubuwan dake gudana a Syria. MUna kuma fatan zamu sami hadinkai da Rasha, wadda a karon farko akalla, ta gane bukatar gaggauwa binciko hanyoyin shawo kan halin da ake ciki a kasar ta Syria"

Ga kasashen Turai kuwa, dayadaga cikin abubuwan dake damun su a kudirin na Rasha shine yadda a cikin sa aka daidaita rashin imanin gwamnatin Bashar al-Assad da gwada karfin da kunbgioyoyin adawa suke nunawa a kasar ta Siriya.

Mawallafa: Thomas Schmidt da Umaru Aliyu

Edita: Usman Shehu Usman