An cika shekara guda bayan harin birnin Nice
July 17, 2017Wadannan Limaman dai sun fara tafiyar cikin mota ne daga Cocin Kaiser Wilhelm da ke birnin Berlin, Cocin da a harabarsa ne aka kai harin ta'addancin watan Disamban bara. Inda kuma Limamen suka ratsa birnin Busssels na kasar Beljiyam da Toulous na kasar Faransa sai kuma birnin Nice wanda ya gamu da mummunan harin ta'addanci. Harin da kuma a wannan rana ne ake bikin tunawa da aukuwarsa. Fasto Martin Germer shi ne Limamin Cocin na Kaiser Wilhelm a Berlin, wanda daga nan ne aka fara tattakin. A wata hira da sashin Hausa na DW, yayin taro kan magacen ayyukan ta'addanci wanda makarantar Cocin Evanjilika da ke Hofgeismar, ya bayyana cewa:
Babu ruwan Musulunci da ta'addanci
"Limaman addinin Islaman sun yi gayya ne inda suka fara gangami daga nan Cocinmu, a wani matakin nuna adawarsu ga ayyukan ta'addanci. Wadannan Limaman da suka fara tattakin daga nana Cocin Kaiser Wilhem, sun fito ne daga kasashen Turai daban-daban. Dama sun shirya tattakin zai kare a birnin Nice ne a ranar da ake tunawa da harin ta'addanci da ya rutsa da birnin, kuma ya zo dai-dai da ranar samun yancin kasar Faransa. Wannan mataki ne da Limamen ke son nuna cewa, Musulmai da Yahudawa da Kiristoci su na iya hada kai don yakar ta'addanci a Turai"
Dama dai tun kai hari birnin Berlin, Limamai daga ko wane bangare na kirista da Yahudawa da na Islama, suka kawo ziyarar nuna hadin kai a Cocin na Kaiser Wilhelm, kamar yadda fasto Martin Germer ya bayyana.
"Bayan kai harin washe gari da yamma muka gudanar da addu'o'i, bishop-bishop da fada-fada da sauran manyan Limamen Katholika da na addnin Musulunci da na Yahudu, suka zo muka gudanar da addu'a tare. Inda harabar Cocin Kaiser Wilhelm ta cika makil da mabiya addinai daban-daban, don haka a yanzu mun kasance wata alama ta zaman lafiya."
A yanzu haka dai kasashen Turai sun dau matakai ba iyaka, domin dakile hare-haren ta'addanci, musamman yadda yanzu batun ke neman mamaye kasashen Turai. To sai dai duk da matakan da ake dauka, bai hana 'yan ta'adda samun nasara ba, don haka a yanzu jama'a sun fara dawowa daga rakiyar jami'an tsaron. Don jin dalilin rashin gamsuwar jama'a da matakan tsaro, shi ne yasa a taron wanda makarantar Cocin Evanjilika da ke Hofgeismar ta gudanar, DW ta yi amfani da shi don jin ra'ayin Farfesa Hans-Jürgen Papier, tsohon shugaban kotun tsarin mulki na Tarayyar Jamus.
Yarda tsakanin jami'an tsaro da al'umma na da mahimmanci
"A gani na dai tsarin siyasa na kare al'umma ya na bukatar gyara: Bai kamata ace jami'an tsaro su yi ta tara bayanai kan ko wane dan kasa ba, da sunan ana tuhumar aukuwar harin ta'addanci. Wannan ina ganin shi ya sa jami'an tsaro suke rasa yarda daga jama'a. Ni kaina ina goyon bayan daukan tsauraren matakan tsaro don kare kasa, amma a shawarata, ya kamata masu tattara bayanan su maida hankali kan mutanen da ake tuhuma, kuma ake ganin suna iya zama hatsari ga kasa, amma ba wai kawai kowa ace sai an tattara bayanai kansa ba. Amma fa ace wai 'yan kasa baki daya a yi ta tattara bayanansu bisa amfani da na'urori, wannan duk zai zama jeka na yi ka."
Dama dai tun aukuwar harin ta'addanci a birnin Paris, al'ummar Musulman birnin suka yi gangamin nuna adawa da ta'addanci, haka ma a birnin Kolon na kasar Jamus, kungiyoyin Muslmai sun shirya wani gangami na mutane dubu 10, don yin Allah wadai da ayyukan 'yan ta'adda, wanda ake dangantawa da addinin Islama. Haka suma wadannan Limamai 60 da suka fito daga kasashen Turai daban-daban, suna fatan ganin irin wannan gangami na kai ziyarar jajanta wa ga wadanda hare-haren ta'addanci ya shafa, zai sauya tunanin wadanda ba su fahimci bambanci addinin Islama da 'yan ta'adda ba.