1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cika shekara guda da kaddamar da juyin-juya hali a Masar

January 25, 2012

Dubunan al'umar Masar sun hadu a dandalinTahrir albarkacin cikar shekara guda da fara zanga-zangar da ta kori Hosni Mubarak daga gadon mulki.

A general view shows Egyptian protesters demonstrating of the first anniversary of 25th January uprising in Tahrir square, Cairo, Egypt, 25 January 2012. Protesters gathered in Tahrir square preparing for the anniversary of the revolution. EPA/MOHAMED OMAR +++(c) dpa - Bildfunk+++
Dandalin TahrirHoto: picture-alliance/dpa

Duban al'umar Masar, sun yi dafifi a dandalinTahrir dake birnin Alkahira,domin tuni da cikwan shekara guda daidai, da fara zanga-zangar neman sauyi, wadda ta kifar da shugaban kasa Osni Mubarak, bayan shekaru fiye da Talatin da ya share kan karagar mulki.

Saidai masu zanga-zangar sun yi ta rera kalamomi, inda suke bayyana bukatar sojoji su gaggauta sauka daga karagar mulki.Daya daga cikin masu masu zanga-zangar ya bayyana dalilinsu na:Sun yi ta cewa za su mika mulki, amma har yanzu ba mu gani a kas ba,a yanzu maganar gaskiya itace, kasar Masar na cikin mulkin kama karya na sojoji.

Wannan bikin cikon shekara guda, ya zo kwana daya kacal, bayan da aka rantsar da sabuwar Majalisar Dokoki, wadda a cikin ta jam'iyu masu kishin addinin Islma suka samu rinjaye.Sannan a jiya, sojojin kasar Masar, sun dade dokar ta bace wadda aka girka yau shekaru fiye da talatin da suka wuce.

Mawallafi:Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu