1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cika shekaru 10 da sace daliban Chibok

April 14, 2024

A wannan Lahadin ce aka cika shekaru goma da sace 'yan matan Chibok a jihar Bornon Najeriya, sai dai har yanzu akwai kusan dalibai dari da ba a samu cetowa ba, batun da ke ci gaba da daga hankalin iyayensu.

Shekaru 10 bayan sace daliban Chibok
Hoto: Audu Ali Marte/AFP

 

Ranar 14 ga watan Afrilun shekara ta 2014 ce aka sace dalibai makaranta Chibok 276 wadanda shekarunsu suka kama daga15 zuwa 18 yayin da su ke rubuta jarrabawa karshe ta kammala sakandare.

Labarin satar daliban dai ya ja hankalin duniya inda kungiyoyin da sauran masu gwagwarmaya ga ma hukumomi da gwamnatoci kasashen duniya har ma da Majalisar Dinkin Duniya su ka yi ta fafutukar ganin an sako su domin komawa ga iyayensu. Daga cikin wadanda aka sace akwai kusan ‘yan mata 164 da su ka kubuta ko aka sake su bisa wata yarjejeniya, sai dai har yanzu akwai wasu da dama da ke hannun 'yan bindigar yayin da ake fargabar wasu sun mutu.Boko Haram ta aura wa kanta sama da 'yan matan Chibok 20

Wannan yayin da yaran ke ciki dai ya haifar da shiga yanayi na dimuwa daga bangaren iyayen yara, musamman ma wadanda kawo yanzu ba su dawo ba. Malam Ayuba Alamson da ke magana da yawun iyayen daliban Chibok din ya ce bakin cikin da suka ciki ba zai misaltu ba inda ya kara da cewa ''kowane lokaci kuka muke kuma muna zaman zullumi. Bakin cikin da muke ciki ba zai misaltu ba.''

Yanzu haka dai an koma harkokin karatu gadan-gadan a wannan makaranta bayan sake ginata da hukumomi su ka yi, inda shugaban makarantar na yanzu Muhammad Bukar Chiroma ya ce ''makarantar a yanzu ta kunshi maza da mata kuma ya kara da cewa harkokin karatu sun samu ci gaba sosai, malaman da muke da su ma su na kokari sosai. Iyaye kuma na ganin haka din har suna dauko 'ya'yansu daga wasu makarantu suna kawo su wajenmu.'''Yar Chibok ta koma ga iyayenta bayan shekaru 7

Duk da cewa lamura sun daidaita a garin na Chibok sannan ana ci gaba da karatu, wasu na ganin bai kamata a ja kafa ba wajen ci gaba da yunkuri na kubutar da wadanda har yanzu suke hannu. Maryam Wabi da ke cikin wandada suka tsira ta ce daliban na neman hukumomi su basu agaji. A hirarta da DW ta ce ''muna neman taimako don mu samu abin da zai sa mu manta da wahalar da muka sha''.