Jamus za ta sake duba batun 'yan cirani
July 3, 2018![Auftakt Klausur CSU-Landesgruppe](https://static.dw.com/image/39633612_800.webp)
Talla
A jiya litinin ne dai Shugabannin jam'iyyar CDU ta Angela Merkel da kuma jam'iyyar CSU wadda Horst Seehofer ke jagoranta suka gana a birnin Berlin don nemo bakin zaren rikicin dake shirin ballewa a fadar mulkin kasar, bayan da ministan cikin gida yayi barazanar sauka daga kujerar sa matukar Merkel din ba ta dauki matakin gaggawa kan bakin da suka kasar ta Jamus ba.