1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Chadi: An cimma yarjejeniyar zaman lafiya

Mouhamadou Awal Balarabe RGB
August 8, 2022

Gwamnatin rikon kwaryar Chadi da kungiyoyin 'yan tawayen kasar ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a birnin Doha na kasar Katar a wannan Litinin.

Katar Der Vorsitzende des Militärischen Übergangsrates des Tschad, Mahamat Idriss Deby, trifft den Emir von Katar, Scheich Tamim bin Hamad Al Thani
Hoto: Amiri Diwan of the State of Qatar/Handout/AA/picture alliance

Gwamnatin rikon kwarya ta kasar Chadi da kungiyoyin 'yan tawaye sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a birnin Doha a wannan Litinin, gabanin babban taron sulhu na kasa da zai gudana a karshen wannan wata na Agusta da muke ciki. Bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar, ya biyo bayan tattaunawar da aka yi na tsawon watanni a babban birnin na Katar, a tsakanin bangarorin da ke gaba da juna. 

Jagoran mulkin sojan Chadi Mahamat Idriss Deby Itno da kansa ne ya yi takakki zuwa birnin Doha domin rattaba hannu kan yarjejeniyar da kungiyoyin 'yan tawaye fiye da talatin, suka amince da shiga tattaunawar kasa. Amma ba a fitar da cikakkun bayanai kan yadda za a aiwatar da yarjejeniyar da kuma yadda za a bi diddiginta ba.

Masu adawa da juna sun cimma matsayaHoto: Mahamat Idriss Déby Itno/Facebook

Mahamat Zene Cherif, ministan harkokin wajen Chadi ya ce, ya yi imanin cewa yarjejeniyar za ta kai ga samar da zaman lafiya mai dorewa a kasar Chadi saboda ta hada akasarin bangarorin da ke gaba da juna.

“Abin da ke da muhimmanci shi ne sakamakon da muka samu bayan tsawon lokaci na tattaunawa, kuma ina ganin cewa wannan yarjejeniyar, za ta kai mu ga samun zaman lafiya mai dorewa a kasar Chadi"

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce, wadanda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sun amince da tsagaita bude wuta tare da yin aikin kwance damarar yaki. Hakazalika gwamnatin mulkin soji ta  Chadi ta kuduri aniyar daina kaddamar da samame  a kan kungiyoyin 'yan tawaye da suka samu mafaka a kasashen da ke makwabtaka da ita.

Shugaban riko, Mahamat Idriss DebyHoto: Christopeh Petit Tesson/AFP/Getty Images

Gwamnatin mulkin soja tana karkashin jagorancin Mahamat Idriss Deby, wanda a shekarar da ta gabata ya kwace mulki bayan mutuwar mahaifinsa.

Da farko, majalisar gudanarwarsa ta ce, za ta mika mulki ga farar hula bayan rikon kwarya na tsawon watanni 18, amma babu alamun shirya zaben kasancewar wa'adin na karatowa ba tare da an warware rikicin cikin gida ba.

A yayin da yake magana a wajen rattaba hannun kan yarjejeniyar, ministan harkokin wajen Katar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al-Thani, ya yi kira ga kungiyoyin da ba su sanya hannu ba, da su shiga a dama da su. 

Biyu daga cikin wadanda ke da ruwa da tsaki a rikicin na Chadi ba su halarci taron rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar ba, ciki kuwa har da Mahamat Mahdi Ali da ke zama shugaban FACT.

Dama kungiyar ta 'yan tawaye tana daya daga cikin wadanda suka kai harin da ya yi sanadin mutuwar Marshal Idriss Deby Itno, wanda ya shafe shekaru talatin yana mulkin kasar Chadi. Cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta FACT ta ce, ta ki sanya hannu kan yarjejeniyar, saboda burus da aka yi da bukatunta, ciki har da membobinta da ke tsare. Amma ta yi ikirarin cewa tana shirye ta shiga tattaunawa a ko da yaushe.

A lokacin da yake bayyana ra'ayinsa, babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya danganta yarjejeniyar da muhimmin ci-gaba ga al'ummar Chadi, tare da nuna bukatar hadin kan kowa da kowa don samun nasara a taron kasa.

Shi kuwa shugaban hukumar zartarwa ta KungiyarTarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat dan asalin kasra ta Chadi, ya yi alfahari da yarjejeniyar yin sulhu don zaman lafiya saboda a cewarsa, za ta iya magance rarrabuwar kawuna da ta zama ruwan dare a Chadi.