An daga turar Sweden a harabar shedikwatar NATO
March 11, 2024A wannan rana ta Litinin 11 ga watan Maris 2024, aka daga tutar kasar Sweden a harabar shedikwatar NATO, da hakan ya bude sabon babin kungiyar ta NATO da kuma hakan ya kai mambobin kungiyar zuwa 32.
Karin bayani: Sweden ta zama memba na 32 na kungiyar NATO
Wasu hotunan kamfanin dillancin labarai na AFP ya nuna Firaiministan Sweden Ulf Kristersson da Sakatare Janar na NATO Jens Stoltenberg har ma da gimbaya mai jiran gado ta kasar Denmark Victoria na kallon yadda sojoji ke daga tutar ta Sweden a wani kwarya-kwaryan biki da aka gudanar a birnin Brussels na kasar Belgium.
Karin bayani: Matakin karshen na shigar da Sweden cikin NATO
Sweden ta dauki matakin da ya dace kuma a lokacin da ya dace, a cewar Sakatare Janar na NATO Mr. Stoltenberg tare da Firaiministan Sweden.
Karin bayani: Finland ta jaddada kudirinta na shiga NATO
Kasashen Sweden da Finland da ke kasancewa 'yan ba ruwanmu a al'amuran da suka shafi NATO tun bayan yakin duniya na II, sun mika bukatar shiga kungiyar a watan Mayun 2022.