1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

An dage babban zaben Libiya

Abdoulaye Mamane Amadou
October 6, 2021

Shugaban majalisar dokokin Libiya na rikon kwarya Abdallah Blihek ya sanar da dage zaben 'yan majalisun dokoki da na shugaban kasa har zuwa watan Janairun sabuwar shekara.

Libyen Premierminister Abdul Hamid Mohammed
Hoto: Hazem Ahmed/AP Photo/picture alliance

 A ranar 24 ga watan Disamban wannan shekara ne aka kayyade za a gudanar da zaben ‘yan majalisar da na sghugaban kasa, zaben da ke da matikar muhimmanci wajen kawo karshen yakin basasa da rudanin siyasar da Libiyar ta jima a ciki tana fama da su.

Tun da jimawa, bangarorin biyu masu karfin fada a jin a fagen siyasar Libiya wato majalisar dokokin da ke Toubrouk a gabashin kasar da ta majalisar koli da ke gudanar da sha'anin mulkin da ke da matsayin majalisar dattikjai mai da mazauni a birnin Tripoli, ke samun mabanbantan ra'ayi kan batun tsara zaben gama gari.