An dage dokar ta baci a Pakistan
December 15, 2007Talla
Shugaban ƙasar Pakistan Parvez Musharraf ya ɗage dokar ta ɓaci da ya kafawa ƙasarsa a farkon watan Nuwamba. Musharraf ya ce kafa dokar ya zama wajibi saboda a cewarsa kwantar da rikicin da ya so tashi a ƙasar tare kuma da dakatar da fannin sharia gurgunta harkokin gwamnati. An dai shirya a watan Janairu mai kamawa za a gudanar da zaɓe da ake sa ran jam’iyun abokan hamaiya biyu wato tsoffin firaminista Nawaz Sharif da Benazir Bhutto zasu shiga. A halin da ake ciki kuma wani harin ƙunar bakin wake da aka kai kusa da wani sansanin soji a arewa maso gabashin ƙasar ya halaka mutane akalla biyar.