1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An dakatar da ganawar Trump da Putin

October 22, 2025

An dakatar da taron da ake sa ran gudanarwa tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da shugaban Rasha Vladimir Putin a birnin Budapest na kasar Hungary.

Shugaba Trump na Amurka da Vladimir Putin na Rasha
Shugaba Trump na Amurka da Vladimir Putin na RashaHoto: ZED

Rahotanni sun nuna cewa an jinkirta taron koli a tsakanin shugaban Amurka Donlad Trump da takwaransa na Rasha Vladimir Putin ne bayan watsin da Rasha ta da shawarar dakatar da yaki da take yi da Ukraine.

Wannan bayani ya fito ne daga ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, bayan tattaunawarsa ta waya da takwaransa na Rasha, Sergei Lavrov.

Shugaba Donald Trump ya tabbatar da batun, yana mai cewa ba ya son zama cikin taro marar amfani da ma bata lokaci.

Daga nata bangaren kuwa, gwamnatin Rasha ta ce shirye-shiryen taron na tafiya, sai dai akwai bukatar cimma matsaya kan wasu muhimman batutuwa kafin a ci gaba.

Daga bisani dai, fadar Kremlin ta fitar da sanarwa, tana jaddada cewa sharuddan da ta gindaya domin cimma zaman lafiya a Ukraine, ba su sauya ba.