An dakatar da taron gangamin adawa a Kenya
January 3, 2008Jam´iyyun adawa a Kenya,sun dakatar da taron gangami da su ka shirya gudanarwa yau. Matakin a cewar Jam´iyyun, nada nasaba ne da ƙoƙarin kawo ƙarshen asarar rayuka ne. Mutane sama da ɗari uku ne a yanzu haka akayi asarar rayukansu, sakamakon zanga-zangar adawa da Gwamnati. Jam´iyyun sun shirya wannan gangami ne na yau, don adawa da sakamakon zaɓen daya bawa Mwai Kibaki nasara. Ko kafin ɗaukar wannan mataki, Gwamnatin ƙasar ta hana ´yan adawar gudanar da wannan zanga-zanga. Mr Raila Odinga daya ƙalubalanci Kibaki a wannan zaɓe, ya tabbatar da cewa Gwamnati ta yi amfani da ƙarfin mulƙi, wajen sace wannan zaɓe ne. A mako mai zuwa ne Jam´iyyun adawar su ka shirya gudanar da taron gangamin, dangane da adawa da sakamakon wannan zaɓe na shugaban ƙasa.