An dakatar da tattaunawar Siriya
February 4, 2016 Manzon MDD a Siriya Staffan de Mistura, ya fadawa wa manema labarai cewa, wakilan taron za su tafi woni dan hutu, tunda babu alamun samun woni ci-gaba. Bisa ga dukkan alamu dai tattaunawar magance yakin basan kasar ta Siriya da aka fara a Geneva ya ruguje. Inda Mistura ya yi karin haske.
"Tun ranar bude tattaunawar na fada cewa, ba mu zo nan don surutu kawai ba, don kawai muna son yin surutai. Kuma shi ma sakatare janar na MDD abinda ya fada ke nan"
'Yan tawayen da ke halaltar taron wadanda kasashen yankin Gulf da Turkiya ke marawa baya, sun janye ne bisa sharadin sai Rasha ta bar kai hari a birnin Alleppo da sauran yankuna dake hannunsu. Ita kuwa gwamnatin Siriya ta yi watsi da bukatar, inda wakilin kasar Siriya a tattaunawar Bashir Jaafari ya zargi makobtan kasashensu, da yin sanadin rushuwar tattaunawa da aka fara. Yayinda su kuwa 'yan tawaye suke cewa kamata yayi Rasha ta rika kai hari wa kungiyar IS, bawai yankuna da ke hannunsu ba.
Yanzu dai fata ta karshe da ake jira kan wannan yaki dake lakume rayuka, ita ce ganawar da dukkan kasashe iyayen wakilan da suka je taron. Inda ake saran a watan gobe kasashen Amirka, Rasha, Iran da Saudiyya za su hallara a birnin Munich na kasar Jamus karkashin kungiyar tuntuba kan rikicin Siriya.