1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin Pakistan ramuwar gayya ce

Zainab Mohammed Abubakar
January 31, 2023

Kwararru a fannin tsaro sun ce sakaci a bangaren tsaro ne ya janyo harin birnin Peshawar da ya halaka rayuka wajen 100 mafi yawa jami'an 'yan sanda.

Pakistan | Explosion in einer Moschee in Peshawar
Hoto: MAAZ ALI/AFP/Getty Images

Duk da wannan zargin, wani babban jami'in 'yan sanda ya bayyana harin kunar bakin wake da aka kai a wani masallaci da ke cikin hedkwatar 'yan sandan na Peshawar a matsayin ramuwar gayya saboda yaki da ta'addanci da jami'an 'yan sandan ke yi a fadin Pakistan.

'Yan sanda tsakanin 300 zuwa 400 ne suka hallara domin yin sallar la'asar a masallacin da ke cikin babban birnin lardin Peshawar a jiya Litinin din, yayin harin da ya rusa katafaren katangar masallacin da akasarinsa ya kone, tare da zubar da baraguzan a kan jami'an.

Babban jami'in ‘yan sandan birnin Muhammad Ijaz Khan ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, sun mike tsaye wajen yakar ‘yan ta'adda, dalili kenan da ya sa aka kai musu harin.

Sai dai masana na danganta mummuna harin da sakaci a bangaren jami'an tsaron.