An dauki matakan farfado da ilimi a Somaliya
July 30, 2013Shekara da shekarun da aka kwashe na rikicin kasar Somaliya, ya janyo rushewar tsarin ilimin kasar. Wani binciken Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa kimanin kashi 40 cikin 100 na yaran kasar ke zuwa makaranta, wato kashi daya bisa uku na yaran. Amma yanzu da aka fara samun zaman lafiya kungiyoyin agaji da suka hada da na Jamus sun fara taimakawa.
A wata makaranta da ke Mogadishu babban birnin kasar ta Somaliya: Ana gudanar da taron safe na dalibai, yara suna karatu a cikin azuzuwa cikin yanayi mai kyau. Tun shekaru biyu da suka gabata lamuran ke sauyawa, akwai masu ba da gudumawar gyara wadannan makarantu.
Yanzu Hassan Adawe Ahmed Darakta wannan makaranta ya karbi baki na kungiyar ba da agaji, wadanda suka taimaka wajen gyaran azuzuwa. Ga kuma abin da yake cewa:
"Nan inda kuke tsaye azuzuwa biyar ne da aka gyara. Farkon wannan shekara mun sake samun wasu bakwai masu kyau. Wadannan kudaden gyara suna fitowa ne daga kungiyar DBG ta Somaliya, wadda ke taimakawa wajen sake gina makarantun da suka lalace. Tun bayan shekara ta 2011 an yi gyara ga kofofi da tagogi masu yawa."
An saka sabbin fitulu da kujerun zama masu launukan kore da shudi. Wannan kungiya ta DBG ta Somaliya da ke gudanar da aikin, tana samun tallafi daga kungiyoyin taimakon raya kasa na Jamus na Caritas da Diakonie gami da gwamnatin ta Jamus.
Muddun da Somaliya tun fil-azal tana cikin kwanciyar hankali da wannan makaranta tana dauke da yara 3000, amma yanzu a zahiri yara 600 ke halartar makarantar. Haka ya kasa adadin da ake bukata. Sai dai akwai mutane masu yawa da suka tserewa rikicin kasar. Amma tun shekara guda da ta gabata lamura sun fara sauyawa na samun zaman lafiya, bayan kwashe fiye da shekaru 20 babu wata tsayayyiyar gwamnati. Makarantu irin wadda Hassan Adawe Ahmed ke jagoranta duk sun sufa, saboda babu wata gwamnati cikin shekaru 18. Maryam Saleban Abokor tana cikin wadanda suka yi amfani da wannan taimako domin kawo sauyi cikin al'umma:
"Na samu wannan tunanin ne ganin yadda yara babu abin da suke yi sai gagaramba a gari. Tun lokacin da gwamnati ta rushe, shi kenan sai aka rufe makarantu. Mun yi tunanin cewa yaran ka iya fadawa cikin aikata miyagun laifuka. Idan babu wani abin da suke yi ko kuma suka koya, saboda haka na yi shawara da iyaye, na shaida musu yadda za mu iya gyara makarantar unguwarmu."
Yanzu sannu a hankali lamura sun fara sauyawa kuma kasar ta Somaliya, tana samun tallafi daga bangarori daban-daban, domin ingata harkar ilimi. Taimakon da mahukuntan birnin Mogadishu ke samu na tasiri matuka wajen bunkasa ilimi.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu