An daure dan jarida shekaru uku a Turkiyya
November 21, 2017Talla
Kotun ta kama dan jarida Oguz Guven da laifuka biyu, da suka hada da yada farfagandan 'yan ta'addan kasashen ketere kuma yin alaka da kungiyar Fetula Gulen malamin da gwamnatin Turkiyya ta zarga da yunkurin kifar da gwamnatin shugaba Racceb Tayyib Erdogan a shekarar 2016, zargin da malamin ya musanta.
Wannan dai ba shi ne karon farko da gwamnatin Turkiyya ke fakon gidan jaridar Daily mai yada labarabarai a yanar gizo ba, abin da 'yan kasar ke kalubalantar gwamnati na neman sawa 'yancin fadin albarkacin baki takunkumi.
A yanzu dai akwai 'yan jaridu 170 na tsare a gidajen yarin kasar Turkiyya, wannan ya sa wani rahoton baya-bayannan kan 'yancin 'yan jaridu a duniya ya nuna Turkiyya a mataki na 155 a jerin kasashen duniya 180.