1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaMasar

Kotu a Masar ta yanke wa madugun 'yan adawa hukuncin dauri

September 16, 2023

A daidai lokacin da aka kada kugen siyasa a kasar Masar, wata kotu ta yanke wa dan adawa hukuncin zaman kaso, tare da cinsa tarar kudi bayan zargin aikata laifi

Masar I Shugaban kasa I Abdel Fattah al-Sisi
Masar I Shugaban kasa I Abdel Fattah al-SisiHoto: Ahmad Hassan/AFP/Getty Images

Wata kotu a Masar ta yanke wa madugun 'yan adawan masu sassaucin ra'ayi Hicham Kassem hukuncin dauri na watanni shida a gidan yari, abin da ka iya haramta masa gudanar da yakin neman zaben shugaban kasa wanda da za a yi a watanni masu zuwa.

Karin Bayani: Kyakkyawan fata bayan shigar Masar a BRICS

Wata majiya daga makusantan dan siyasan ta ce an yankewa Hicham hukuncin zama a gidan wakafi na watanni uku, tare da cinsa tarar kudi Yuro 600 bisa zarginsa da yin kalaman karya kan wani minista a lokacin da ya gurfana a gaban kotu.

Karin Bayani: Haramcin sanya nikabi a makarantun Masar

Tuni lauyan da ke kare dan siyasa Nasser Amin ya sanar da daukaka kara kan hukuncin, inda ya ce za a sake zaman shari'ar a farkon watan Oktoba. Wannan dai ba shine karon farko da wani dan adawa a Masar ke fuskantar shari'a ba tun bayan da aka buga kugen siyasa a kasar.