1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An daure mai dakin hambararren shugaban Gabon

October 12, 2023

Rahotanni daga Gabon na nuni da cewa, an aika da mai dakin hambararren shugaban kasar Ali Bongo zuwa gidan yari bisa zargin ta da yin sama da fadi da wasu kudade.

Shugaban kasar Gabon, Ali Bongo da mai dakinsa, Sylvia Bongo Ondimba
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Reynolds

Lauyan Sylvia Bongo Ondimba ya bayyana tsare ta a matsayin abin da ya sabawa doka. Ana dai zargin dattijuwar mai shekaru 60 da laifin halasta kudin haram da kuma lalata bayanan sirri.

Kafafen yada labaran kasar sun ruwaito cewa, ana tsare da ita a gidan yari babban birnin kasar Libreville bayan an dade ana saurarar karar a gaban alkali.

Karin bayani: Sojoji sun yi juyin mulki a Gabon

Jagororin juyin mulkin Gabon, sun zargi Sylvia da amfani da matsayin mai gidanta wanda ba shi da cikakkiyar lafiya wajen yin gaban kanta, inda ita da guda daga cikin 'ya'yansu suka rika almubazarranci da kudaden jama'ar kasar da ke da arzikin mai.

Karin bayani: Gabon: Iyalan Bongo na shugabancin gado

Tun bayan juyin mulkin ranar 30 ga watan Agustan wannan shekarar ce, aka yi wa Slyvia Bongo daurin talala, bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin farar hula da ya kawo karshen mulkin shekaru 55 na ahalin gidan Bongo.