Kotu ta daure wasu 'yan jam'iyyar adawa
August 9, 2019Talla
Kotun ta Kamaru daure wasu magoya bayan jam'iyyun adawa kimanin 40 har tsawon wa'adin watanni shida-shida a gidan yari, sakamakon kamasu da aikata laifin zanga-zangar nuna kyama ga sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Oktoban shekarar bara, a yain da lauyan da ke kare jam'iyyar a yankin na Douala ya ce akwai yiwuwar daukaka kara idan har jam'iyyar adawar ta kammala cikakken nazari.